Roger Waters ya ce Trump alade ne

Shahararren mawakin kasar Ingila Roger Waters,kana shugaban kungiyar makidan Rock, Pink Floyd ya shirya wani zazzafan casu a birnin Saint Petersburg na kasar Rasha don yaka rigar mutuncin Donald Trump.

Waters ya cashe a fagen wasa tare da wakarsa ta farko mai suna "Charade",wacce ta yi matukar daukar hankalin masoyansa.

A wata waka ta daban da ya rera, mawakin ya nuna hotunan trump sanye da tufafi nmata.

Bayan ya kammala wakarsa, sai ya rubuta wata jumla a wani makeken allo da ke bayansa kamar haka : "Trump alade ne".

A ranar 13 ga watan Agustan bana ma, Waters ya caccaki shugaban na Amurka,wanda ya kira da ci-ma zaune.

A wani bayani da yayi a kafar yada labarai ta RT, mawakin ya ce,

"Babu wata tsiyar da Trump ya yi, face sake kulla alaka da kasar Rasha".

Tag: alade , casu , rasha , waka , trump

Labarai masu alaka