Schweinsteiger ya yi bankwana da kwallon kafa

Dan wasan tsakiyar Jamus na kwallon kafa Bastian Schweinsteiger ya sanar da barin harkokin kwallon kafa a rayuwarsa.

2018-08-28T204636Z_286638510_RC1EF25A5370_RTRMADP_3_SOCCER-GERMANY.JPG
2018-08-28T203150Z_1121250386_RC1AAAB65720_RTRMADP_3_SOCCER-GERMANY.JPG
2018-08-28T195818Z_1509264436_RC1D076D9FE0_RTRMADP_3_SOCCER-GERMANY.JPG

Dan wasan tsakiyar Jamus na kwallon kafa Bastian Schweinsteiger ya sanar da barin harkokin kwallon kafa a rayuwarsa.

Schweinsteiger wanda daya ne daga cikin kwararrun 'yan wasan Jamus ya buga wasan bankwana da aka shirya wanda Bayern Munich ta karbi bakuncin Chicago Fire wadda daya daga cikin manyan kungiyoyin Amurka ne.

An buga wasan a filin wasanni na Allianz inda 'yan kallo dubu 75 suka kalla.

Shekaru 13 kenan da Schweinsteiger ya ke taka leda a kungiyar Bayern Munich inda a wasan bankwanan ya buga wa kowanne bangare.

Ya jefa wa Bayern Munich kwallaye 4 a wasan da ya buga na karshe.Labarai masu alaka