• Bidiyo

Maduro: Afirka ce ta lashe gasar kwallon kafa ta duniya ta FIFA ta 2018

Shugaban Kasar Venezuela Nicolas maduro ya bayyana cewa, nahiyar Afirka ce ta yi nasarar lashe gasar cin kofin duniya ta kwallon kafa ta FIFA da aka yi a Rasha.

Shugaba Maduro ya yi jawabi a wajen wani taro da aka gudanar a Kasarsa cewa, "kungiyar kwallon kafa ta Faransa ce ta lashe kofin duniya amma kuma kungiyar na kama da ta Afirka. Asali dai Afirka ce ta fi nasara. 'yan wasan 'ya'yan wadanda suka yi gudun hijira zuwa faransa daga Afirka ne."

Ya ce, yana fata a kasashen Turai za a daina nuna bambanci da wariya gta 'yan Afirka tare da daina kyamar 'yan gudun hijira.

Shugaban na Venezuela ya ci gaba da cewa, "suna kallon Afirka a matsayin waje mai wahala. Sun sace arzikin nahiyar. kuma sai ga shi a gasar cin kofin duniya Faransa ta yi nasarar lashe gasa sanadiyyar 'yan wasan 'yan asalin Afirka."

Maduro ya kuma taya Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin murnar masarar da ya yi wajen karbar bakuncin gasar cikin nasara.Labarai masu alaka