Ronaldo: Ina son kafa tarihi a Juventus

Shahararren dan wasan kwallon kafa na duniya dan kasar Portugal Christiano Ronaldo ya bayyana cewa, yana son kafa tarihi a kungiyar kwallon kafa ta Juventus da ya sanya hannu da ita bayan ya bar Real Madrid.

Ronaldo ya zanta da manema labarai a filin wasa na Allianz da ke Torino a Italiya inda ya ce, yana son ya kafa tarihi a wannan kungiya ta Juventus.

Ya ce, kowa yana ta hankoron nasarar lashe gasar Zakarun Turai ta UEFA ama shi zai yi gwagwarmaya don lashe dukkan kofuna.

Ronaldo ya kuma ce, a yanzu ya bude sabon shafi a rayuwarsa ta sanar’ar kwallon kafa.

Dan wasan dai ya sanya hannu na shekaru 4 da Juventus ta Italiya bayan ya bar Real Madrid ta Spaniya.Labarai masu alaka