"Hukunci ya tabbata ga 'yan wasanmu da suka kunyata mu a idan duniya"

Shugabannin Saudiyya sun lashi takobin hukunta 'yan wasan kwallon kafa na kasarsu,wadanda takwarorinsu na Rasha suka lallasa da ci 5 da nema.

"Hukunci ya tabbata ga 'yan wasanmu da suka kunyata mu a idan duniya"

Shugabannin Saudiyya sun lashi takobin hukunta 'yan wasan kwallon kafa na kasarsu,wadanda takwarorinsu na Rasha suka lallasa da ci 5 da nema.

Shugaban hukumar kwallon kafar Saudiyya, Abdel Azzat ya ce,

"A gaskiya muna matukar bakin cikin yadda aka buga wannan wasan.Saboda kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.Mun share lokaci mai tsawo muna shirya wannan gasar.Za a ci tarar 'yan wasa da dama,wadanda suka hada da Muhammad Al Sahlawi, Umar Hausawi da mai tsare raga Abdullah Al Mayuf".

Shugaban hukumar kula da wasannin motsa jiki ta Saudiyya,Turki al Sheikh ma, ya daga murya ga wannan abin kunyar,inda ya ce,

"'Yan wasan sun ba ni kunya matuka gaya.Wannan ai abin takaici ne.Wannan shi ne kontiragen da muka rattaba wa hannu don gayyatar kwararrun kocinan duniya ? Babu abinda bamu yi wa 'yan wasanmu ba.Mu dauki dukannin dawainiyarsu tsawon shekaru 3.Mun gayyato manyan kocinan duniya,amma basu nuna mana daidai kashi 5 cikin dari na abinda muke bukatar gani daga gare su ba.Wannan abu ne da kowa ya kamata ya san da shi".

Turki ya kara da cewa,

"Sai mun maka ma'aikatan tashar talabijin kasar Qatar kotu,wadanda suka dinka mara wa 'yan wasan Rasha baya da kuma aibanta Saudiyawa.Sun yi amfani da wannan damar don yi mana bita-da-kulli kan matsalar siyasar da ke tsakanin kasashenmu.Shugabannin Saudiyya sun yi gaskiya da suka dakatar da shirye-shiryen wannan tashar a kasarmu"

 Labarai masu alaka