Za a shirya fim game da rayuwar Bob Marley

Babban kamfanin shirya fina-finai na Paramount Pictures da Ziggy Marley zasu hada karfi da karfe don shirya fim game da rayuwar daya daga cikin fitattun mawakan duniya,marigayi Bob Marley.

Ziggy Marley babban dan Bob Marley ya fara gudanar da aiki tukuru don shirya fim game da rayuwar gyatuminsa.

A fim din za a gabatar wa masu kallo cikakken labarin mashahurin mawakin.

Kawo yanzu an ki a bayyana sunayen taurarun da zasu taka rawa a wannan sabon fim,wanda zai kunshi dukannin wasu labaran gaskiya da aka taba bayarwa kan mawakin a fina-finan gaskiya da kuma kawo bangarorin rayuwarsa da ba a taba ji ba.

A tsawon shekaru 7 da suka shude,Ziggy Marley wanda ya rungumi sana'ar babansa,ya fitar da fina-finan gaskiya 3 tare da shirya wani gaggarumin shagali da zummar raya gadon mahaifinsa a zukatan matasan duniyarmu ta yau.

Ana kyautata zaton Ziggy Marley, zai kasance a sahun masu bada umarni na wannan fim.Labarai masu alaka