An nuna fim din 'Ar Risâlah' a Saudiyya

Bayan shekaru 35 da haramta kallo,Saudiyya ta bude kofofin gidajen sinima,inda a karo na farko za ta nuna fim din 'Ar Risâlah',wanda ke nuni da rayuwar mafificin halitta.

An nuna fim din 'Ar Risâlah' a Saudiyya

Bayan shekaru 35 da haramta kallo,Saudiyya ta bude kofofin gidajen sinima,inda a karo na farko za ta nuna fim din 'Ar Risâlah',wanda ke nuni da rayuwar mafificin halitta,Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi.

Bayan shekaru 42,Saudiyya ta bada izinin nuna fim din da mashiryi Mustafa Akkad na kasar Amurka dan asalin sham ya shirya a shekarar 1976 tare da taurarun fina-finai na kasashen Larabawa.

Kazalika a Masar,Morocco,Irak,Lubnan da awancin kasashen Larabawa a yankin Gulf, za a nuna fina-finan da suka yi fice a bikin nunan fina-finai na kasa da kasa na Dubai, daga ranar 14 ga watan Yunin bana, a albarkacin sallar Azumi.

Ana kyautata zaton shugabannin Koweit ma, za su yi na'am da wannan matakin na nuna fina-finai.

A lokacin da 'Ar Risâlah' wato "The Message" a Turance ya fito, sarkin Saudiyya na wancan zamanin ya karbe shi da hannun biyu-biyu,amma a shekarar 1979 a lokacin juyin juya halin Musuluncin kasar Iran, gabar da ta kunno kai tsakanin Iran da masarautar da kuma tasirin akidar Wahabiyanci a wajejen shekarar 1980, sun sa uluma'u suka yi watsi da fim din ga baki daya.

A sanadiyyar bacin ransu da manyan malaman duniyar Islama suka nuna a wancan zamanin,maimakon a shirya fim din a farfajiyar Kaaba da kuma biranen Makka da Madinah ba,sai aka shirya shi a Morocco.

A zamanin da ya fito, 'Ar Risâlah'  yayi matukar zama alakakai a kasashen Musulmai da na Turai.

A lokacin da aka kuduri nuna fim shi a Amurka,'yan kungiyar Musulman Amurka da ke birnin Washington,sun far wa gidan sinima,don suna kyautata zaton cewa za a nuna Annabi a fim din,abinda yasa matsaloli daban-daban suka dinka kunno kai.

 Labarai masu alaka