• Bidiyo

An fara gasar Kwallon Badminton ta kasa da kasa a Itopiya

An fara gudanar da gasar kwallon badminton ta kasa da kasa a Addis Ababa babban birnin kasar Itopiya inda 'yan wasa 85 daga kasashe 12 suke halarta.

Kasashen Turkiyya, Itopiya, Uganda, Isra'il, Luxenburg, Zambia, Jordan, Masar, Aljeriya, Sri Lanka, Indiya da Seychelles ne suke halartar gasar ta kwanaki 4.

Gasar ta samu halartar shugaban kungiyar wasan bandminton na Itopiya da sauran manyan jagorori a harkokin wasanni.

Shugaban na harkokin bandminton a Itopiya Gebreeyesus Ayele ya shaida wa manema labarai cewa, wannan ne karo na 7 da kasar ta ke karbar bakuncin irin wannan gasa wadda ta ke da matukar muhimmanci duba da kasashen da suke halarta.

Ya ce, wasan ba bai shahara a Itopiya ba amma ana kokarin yada shi a tsakanin jama'ar kasar.Labarai masu alaka