Galatasaray ta yi bankwana da gasar UEFA Europa

Kungiyar kwallon kafa ta Galatasaray ta Turkiyya ba ta yi karko ba a gasar zakarun Turai ta UEFA Europa inda ta yi bankwana da gasar da wuri.

Galatasaray ta yi bankwana da gasar UEFA Europa

Kungiyar kwallon kafa ta Galatasaray ta Turkiyya ba ta yi karko ba a gasar zakarun Turai ta UEFA Europa inda ta yi bankwana da gasar da wuri.

A wasa na 2 da kungiyar ta buga da takwararta ta Swidin Östersunds an tashi 1 da 1.

An buga wasan a filin wasa na Turk Telekom da ke Istanbul.

Östersunds  ta jefa kwallonta 1 ta hanyar bugun daga aki sai mai tsaron gida a minti na 60 ta hannun dan wasanta Brwa Nouri. 

Galatasaray kuma ta jefa tata kwallon a minti na 69 ta hannun Ahmet Çalık.

Galatasaray ta yi rashin nasara da ci 2 da nema inda a yanzu ta yi bankwana da gasar.Labarai masu alaka