• Bidiyo

Duk wani mai laifi ba zai so zama a China ba

Kamar yadda ta saba, China ta kara bai wa duniya mamaki,inda a wannan karon ta samar wa 'yan sandan kasarta da wasu gilasai masu siddabaru don gano duk wani tantiri mai mugun nufi.

Wadannan gilasan na kunshe da wata manhajar da ke loda bayanai daga idanun 'yan sanda zuwa ma'adinan bayanai na wasu manyan na'urori masu kwakwalwa dake a helkwatar 'yan sanda, a cikin kiftawar ido.

A yanzu haka, gilasan sun taimaka a wajen cafke wasu miyagu 7.

Wannan sabuwar fasahar, za ta taimaka haikan a wajen karfafa mulkin kasar Sin.