Haɓakar sufurin fasinjoji ta jiragen sama a lstanbul

Sabuwar filin tashi da saukar jiragen saman birnin lstanbul ya yi sufurin fasinjoji na ciki da waje har  dubu 56 da ɗari 420 a farkon watan wannan shekarar.

Haɓakar sufurin fasinjoji ta jiragen sama a lstanbul

Sabuwar filin tashi da saukar jiragen saman birnin lstanbul ya yi sufurin fasinjoji na ciki da waje har  dubu 56 da ɗari 420 a farkon watan wannan shekarar.

Hukumar kula da ayyukan filayen tashi da saukar jiragen sama a Turkiyya (DHMl) ta bayyana cewar sabuwar babbar filin tashi da saukar jiragen saman ta samu ƙarin yawan fasinjoji a wannan watan idan aka kwatanta da na bara.

Filin tashi da saukar jiragen saman Atatürk ya yi sufurin fasinjoji na cikin gida har miliyan daya da dubu 400 da ɗari 790 daga waje kuma miliyan uku da dubu 813 da 23, a jumlace fasinjoji miliyan 5 da dubu 118 da kuma 813.

Filin tashi da saukar jiragen saman Sabiha Gökçen kuwa anyi sufuri fasinjoji miliyan daya da dubu 783 da 145 na cikin gida daga waje kuwa dubu 974 da 701 a watan jiya.

Sabun filin da aka buɗe a ranar 29 ga watan Oktoba a lstanbul a farkon watan shekarar bana ya yi sufurin fasinjoji dubu 59 da 935 na cikin gida, daga waje kuma dubu 32 da 288.

A birnin Istanbul a farkon watan wannan shekarar filayen jiragen saman birnin sun yi hidimar fasinjoji miliyan 7 da dubu 968 da ɗari 882.

ldan aka kwatanta dana farkon watan shekarar bara da aka yi sufurin fasinjoji miliyan 7 da dubu 949 da ɗari 992 an samu ƙarin fasinjoji dubu 8 da 890.

A farkon watan shekarar bana jirage dubu 104 da dari 691 ne suka yi sufuri a faɗin ƙasar Turkiyya.

Kaso 54 cikin ɗari an gudanar dasu ne a birnin Istanbul.

 Labarai masu alaka