Dole ne Musulmai su hade kai

Kakakin gwamnatin Turkiyya,Ibrahim Kalın ya ce kashi 60 cikin dari na fitintinun duniya na afkuwa ne a kasashen Musulmai sakamakon rarrabuwar kawuna,rashin kallon alkibla daya da kuma makauniyar kyama da ke tsakanin su.

Dole ne Musulmai su hade kai

Kakakin gwamnatin Turkiyya,Ibrahim Kalın ya ce kashi 60 cikin dari na fitintinun duniya na afkuwa ne a kasashen Musulmai sakamakon rarrabuwar kawuna,rashin kallon alkibla daya da kuma makauniyar kyama da ke tsakanin su.

Kalın ya furta wadannan kalaman a ranar Jumma'ar nan da ta gabata a albarkacin wani muhimmin taro da aka shirya a cibiyar bincike-bincike kan kididdiga,tattalin arziki,zamantakewa da kuma bada kyaukyawan horo a kasashen Musulmai (SESRIC) da ke Ankara, babban birnin Turkiyya.

Da yake jawabi, kakakin ya ce a yanzu haka wutar tashe-tashen hankula gami rashin tsaro na ci gaba da ruruwa a duk fadin duniya gami.Abinda yasa al'umomin nahiyoyin yammacin duniya,Turai da Latin Amurka na cikin halin kaka-ni-kayi.

"Kashi 60 cikin dari na fintitinun da duniya ke fama da su na afkuwa ne a kasashen Musulmai,wanda hakan ke hargitsa zamantakewar al'umominsu da kuma talautar da su.Wannan wani babban darasi ne.Hanyoyin magance wadannan matsalolin kuma,su ne shugabanci nagari da kuma hadin kan illahirin Musulmai",inji shi.

Daga karshe ya ce,"Musulunci addinin zaman lafiya ne da na fahimtar juna.Ina kiran kasashen duniyar Islama da babbar murya da su hade kai don gwagwarmaya tare tsira tare.A gaskiya abin bakin ciki ne ganin yadda a yau kawunan musulmai suka rarrabu".

 Labarai masu alaka