Turkiyya ta nuna wa Sin yatsa

Shugabannin Turkiyya sun fasata matuka game da yadda gwamnatin gurguzu ta Sin ke ci gaba da take hakkokin Musulman Uygur na kasarta ba sani ba sabo.

Turkiyya ta nuna wa Sin yatsa

Shugabannin Turkiyya sun fasata matuka game da yadda gwamnatin gurguzu ta Sin ke ci gaba da take hakkokin Musulman Uygur na kasarta ba sani ba sabo.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya,Hani Aksoy ya fitar da wata rubutacciyar sanarwa game da gallazawar da Musulman Uygur ke ci gaba da fuskanta a China.

A bayanin Aksoy ya ce: "A kowace rana, gwamnatin gurguzu ta Sin na samar da sabbin dokokin da ke tsunduma Musulman Uygur da sauran takwarorinsu cikin halin ha'ula'i,musamman ma a wadannan 'yan shekaru biyu in ake take hakkokinsu a karara.Abinda yasa kasashen duniya suka fara tada jijiyoyin wuya.Sakamakon yadda lamarin ya wuce gona da iri".

Kazalika ya ci gaba da cewa,"Garkame sama da Musulman Uygur milyan daya a sansanin azabtarwa da na wanke kwakwale,lamari ne wanda a yanzu haka duk duniya ta riga ta shaida.Haka ma sauran Musulman da suka tsalake rijiya da baya ba tsira suka yi ba.Saboda an hana rumtsawa da kuma numfasa daidai da secon daya tak".

"Daruruwan Musulman Uygur wadanda suka yi nasarar yin hijira a kasashen ketare,sun share shekaru da dama ba tare da sun samu wani labari ba game da halin da 'yan uwansu suka kasance a Sin.An raba dubban yara kanana da uwayensu.Sun kasance a halin kadaici da na maraici.Sake dawowa bakin kudurin garkame Musulman Uygur a sansanonin gallazawa babban abin kunya ne musamman ma a wannan karni na 21 miladiya. Mun gana da shugabannin China kan dukannin mumunan da ke ci gaba da afkuwa a yankin Sincan,inda a nan ne yawancin Musulman kasar ke rayuwa."inji sanarwar.

Bugu kari an ce,"Muna matukar bakin cikin mutuwar Abdurrahim Heyit wanda ya kwanta dama bayan shekaru biyu kacal da garkame shi.An dai yanke wa Heyit hukuncin dauri a gidan kurkuku tsawon shekaru 8 sakamakon wata waka da ya rera".

İllahirin wadannan lamurran da ke ci gaba da wakana a yankin Musulman Uygur ya kara fusata shugabannin Turkiyya.

Daga karshe kakakin ya ce,"Muna fatan hukumomin China zasu yi taka tsantsan game da hannunka mai sandar da muka yi musu.Haka zalika muna kiran sakataren janar Majalisar Dinkin Duniya da babbar murya da ya gaggauta daukan matakan dakatar muzgunawar da ake ci gaba da yi wa Musulman Uygur a yankin Sincan na Sin".Labarai masu alaka