Erdogan ya aike da sakon ta’aziyya ga Gani

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya aike da sakon ta’aziyya ga takwaransa na Afganistan Ashraf Gani.

Erdogan ya aike da sakon ta’aziyya ga Gani

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya aike da sakon ta’aziyya ga takwaransa na Afganistan Ashraf Gani.

Majiyoyin Fadar Shugaban Turkiyya sun ce, a sakon na Shugaba Erdogan ya aike da sakon ta’aziyya tare da la’antar harin ta’addanci da aka kai a jihar Vardak.

Sakon na Erdogan ya ce “Shugaban Kasa Mai Girma, Dan Uwana Mai Daraja, na samu labarin harin da aka kai a tsakiyar Vardak a ranar 19 ga Janairu tare da kashe jami’an tsaron Afganistan da yawa da jikkata wasu da dama cikin bakin ciki da bacin rai. Ina la’antar wannan mummunan hari. Ina sake jaddada cewar Turkiyya na tare da ‘yar uwa kuma abokiyarta Afganistan a ko da yaushe wajen yaki da ta’addanci. Ina Addu’ar samun jin kai ga wadanda suka rasa rayukansu da sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata. Ina mika jaje ga jama’ar Afganistan a madadin kaina da al’umata.”

A ranar Litinin din nan ‘yan ta’addar Taliban suka kai harin ta’addanci a jihar Maydan Vardak tare da kashe mutane 126.Labarai masu alaka