Turkiyya ta jajanta wa Mekziko

Shugabannin Turkiyya sun aika sakon gaisuwar ta'azziya ga takwarorinsu na Mekziko sakamakon fashewar da wani bututun man fetur yayi,wanda ya rutsa da rayukan mutane da dama.

Turkiyya ta jajanta wa Mekziko

Shugabannin Turkiyya sun aika sakon gaisuwar ta'azziya ga takwarorinsu na Mekziko sakamakon fashewar da wani bututun man fetur yayi,wanda ya rutsa da rayukan mutane da dama.

Wani bututun man fetur da yayi bindiga a jiya 19 ga watan Janairun shekarar 2019 a yankin Tlahuelilpan na kasar Mekziko ya zama sanadiyyar salwantar rayukan mutane da dama.

A wata rubutacciyar sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ta fitar,shugabannin kasar sun mika gaisuwar ta'azziyarsu ga muhallan kasar Mekziko wadanda a yanzu haka ke cikin alhini.

Sanarwar ta ce : "Mun mika ta'azziyarmu ga 'yan uwan mamata, shugabanni da kuma daukacin al'umar kasar Mekziko.Muna fatan cikakken koshin lafiya ga wadanda suka jikkata a wannan mummunan hatsarin".

Wata mahaukaciyar gobarar da ta afku a jiya bayan fashewar wani bututun man fetur a yankin Tlahuelilpan ya rutsa da rayuka da dama.

A cewar wata sanarwa da shugaban kamfanin albarkatun man fetur Petroleos Mexicanos (Pemex) na kasar Mekziko,yawancin mutane 66 da suka rasa rayukansu a wannan hatsarin sun kasance a gaf da bututun da ya fashe,inda suka je kwasar ganima.

 Labarai masu alaka