Turkiyya ta soki yunkurin juyin mulki a Gabon

Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar da rubutacciyar sanarwar wadda a ciki ta soki yunkurin juyin mulki da aka yi a Gabon.

Turkiyya ta soki yunkurin juyin mulki a Gabon

Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar da rubutacciyar sanarwar wadda a ciki ta soki yunkurin juyin mulki da aka yi a Gabon.

Sanarwar ta zayyana cewa “Turkiyya na sukar duk wani yunkuri na amfani da hanyar da ba ta dace ba wajen kifar da zababbiyar gwamnati.”

Sanarwar ta kuma nuna irin muhimmancin da ke akwai wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Gabon.

A safiyar Litinin din da ta gabata ne wasu sojoji suka kwace iko da gidan rediyon gwamnati na kasa na Gabon tare da sanar da karbe mulki amma ba su yi nasara ba.Labarai masu alaka