Celik: Turkiyya ba za ta saurara ba kan batun samar da tsaro a kan iyakokinta

Kakakin Jam’iyyar AKP mai mulki a Turkiyya Omeer Celik ya bayyana cewa, game a batun tsaro da Turkiyya ke yi, babu wasa, babu sauya lokacin farwa ‘yan ta’adda kuma ba za ta bayar da kai bori ya hau ba.

Bayan taron kwamitin zartarwa na jam’iyyarsa, Celik ya fadi cewar ya kamata da zarar an yi batun abokin aiki to Turkiyya ta zowa kwakwalwar Amurka, amma yadda suke kiran ‘yan ta’adda a matsayin kawayensu abu ne mai bata rai da karya gwiwa.

Celik ya ci gaba da cewar duk mai fadin “Kar ku taba Kurdawa” to ya waiwaya ya kalli madubi.

Ya ce “Su tuna irin zaluncin da suka yi wa Kurdawa. Turkiyya abokiyar Kurdawa, Larabawa da Turkmen dake yankin ne. Tarihi ya nuna yadda a mafi yawancin lokuta Turkiyya ce babbar kawar wadannan mutane. Kar a manta da cewar ba wani da zai ce yana tare da Kurdawa don ya ba wa Turkiyya darussa.Jamhuriyar Turkiyya ita kadai ce abokiyar Kurdawa. Batun tsaro ga Turkiyya abun wasa ba ne, ba abun da za a sauya lokacinsa ba ne, ba abu ne da za a tsaya a na ciniki a kansa ba.”

Tag: AKP , Celik , Turkiyya

Labarai masu alaka