Manyan jami'an tsaro zasu ziyarci Turkiyya daga Amurka

Turkiyya zata karbi manya baki daga kasar Amurka.

Manyan jami'an tsaro zasu ziyarci Turkiyya daga Amurka

Turkiyya zata karbi manya baki daga kasar Amurka.

A safiyar yau mai bayarda shawara na musanman akan tsaron kasar Amurka John Bolton, shugaban rundunar sojan Amurka Joseph Dunford da wakilin Siriya na musanman James Jeffrey zasu kasance a babban birnin Turkiyya wato Ankara.

 

A ziyarar kwanaki biyun da zasu kawo za'a tattauna akan janye sojojin Amurka daga Siriya, yadda za'a ci gaba da kalubalantar kungiyar ta'addar DEASH da sauran muhimman lamurra musanman a fannonin tsaro.

A tattaunawar za'a bayyana ire-iren matakan da sunka wajaba akan Turkiyya.

Za'a kuba aminta akan daukar matakai yadda janye sojojin Amurka daga Siriya ba zai baiwa kungiyoyin ta'addar PKK-YPG da DEASH damar yin kutse a wasu yankunan kasar Siriya ba. 

Haka kuma za'a tabo batun baiwa kungiyar YPG/PKK makamai da Amurka ta yi.

Wanan ziyarar na nuni da cewa shugabanin dakarun kasashen zasu kasance a birnin Ankara lokaci daya.

A taron za'a kuma tattauna akan yadda za'a ci gaba da kalubalantar kungiyar DEASH.

Za'a kuma tabo batun tallafawa dakarun Turkiyya akan sansanin da zasu kafa a Siriya, hadakar da zasu yi da kuma sararin samaniyyar da zasu yi amfani da shi.

 

Za'a kuma mika sakon dake nuni ga yunkurin janye mambobin kungiyar YPG/PKK daga yankin Membich da kuma bin tsarin da aka yi domin dawo da zaman lafiya a yankin da kasar baki daya.

 Labarai masu alaka