Shugaba Erdoğan ya gana da Trump

Shugaba Erdoğan ya gana da takwaransa na Amurka,Donald Trump a wata liyafa da aka shirya a Paris, babban birnin kasar Faransa a albarkacin bikin cika karni daya da tsagaita wutar yankin duniya na farko.

Shugaban na Turkiyya ya kai ziyara Paris a ranar Asabar din nan don amsa goron gayyatar da takwaransa na Faransa,Emmanuel Macron ya aika masa.

An dai shirya liyafar don karrama shugabannin duniya da uwayen gidajensu.

Bayan Trump,shugaba Erdoğan ya gana a asirance da sakataren janar na Majalisar Dinkin Duniya,Antonio Guterres tsawon minti 45.

Tag: paris

Labarai masu alaka