"Dabara ta rage wa mai shiga rijiya"

Shugaba Erdoğan ya ce, a yanzu dai dabara ta rage wa mai shiga rijiya,tunda sun aika wa shugabannin Amurka,Jamus,Burtaniya da Saudiyya bidiyon kisan dan jarida Jamal Kashoggi,wanda a yanzu haka ake ci gaba da neman gawarsa ruwa a jallo.

"Dabara ta rage wa mai shiga rijiya"

Shugaba Erdoğan ya ce, a yanzu dai dabara ta rage wa mai shiga rijiya,tunda a ranar Asabar din nan, sun aika wa shugabannin Amurka,Jamus,Burtaniya da na Saudiyya bidiyon kisan Jamal Kashoggi,wanda a yanzu haka ake ci gaba da neman gawarsa ruwa a jallo.

A baya dai Turkiyya ta tabbatar da cewa,ta tanadi wani faifain rediyo wanda ka iya taimakawa wajen bada cikakken bayani kan mutuwar dan jaridan.

Da yake bayani gaban manema labarai,shugaban na Turkiyya ya ce: "Saudiyya ta san da cewa makasan Kashoggi na a cikin mutane 15 da suka zo Turkiyya kwana daya kacal kafin mutuwar dan jaridan.Kamata ya yi Saudiyyawa su daraja yunkuri da kuma kokarinmu.Shin ko ta ke jira wajen raba dan duma da kabewa ?".


Tag: rijiya

Labarai masu alaka