Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 08.11.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 08.11.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 08.11.2018

Babban labarin jaridar Haber Turk na cewa, Ministan Tsaron Kasa na Turkiyya Hulusi Akar ya bayyana gamsuwarsa game da saka kudi ga wanda ya bayyana inda wani jagoran 'yan ta'addar PKK ya ke da Amurka ta yi, amma kuma an dauki wannan mataki a makare. Akar ya ce, suna son Amurka ta dauki matakan da take dauka kan 'yan ta'addar aware na PKK a kan na YPG dake Siriya.

Babban labarin jaridar Hurriyet na cewa, Tarayyar Turai ta bayyyana cewa, tana goyon bayan dukkan yarjejeniyoyin da ta kulla da Turkiyya. Kakakin Majalisar Tarayyar Turai Margaritis Schinas ta sanar da kamfanin dillancin labaran na Anadolu a yayin wani taron manema labarai da ta kira, a lokacinda aka yi mata tambaya game da Kalaman Mamban Majalisar Johannes Hahn na cewar, akwai bukatar kawo karshen duk wata yarjejeniya da Tarayyar Turai ta kulla da Turkiyya, sai ta ce, abin da Shugaba  Jean-Claude Juncker ya fada kadai ne za a yi aiki da shi. Halayya da Matsayar Tarayyar Turai shi ne ci gaba da aiki tare da Turkiyya.

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, Turkiyya a yayin zaben da aka gudanar a Dubai ta samu kuri'ar kasashen duniya 146 inda ta zama mambar Kungiyar Sadarwa ta Kasa da Kasa. Sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar ta ce, a ranar 5 ga Nuwamba Turkiyya ta zama mamba a Kungiyar wadda Majalisar Dinkin DUniya ta kafa da nufin aiyukan sadarwa tare a tsakanin kasashe. Sanarwar ta ce, a yayin zaben Turkiyya ta samu kuri'u 146 daga kasashen waje.

Babban labarin jaridar Star na cewa, ya zuwa karshen watan Oktoban bana an yi jigilar fasinjoji miliyan 182 da dubu 709 da 862 a Turkiyya a 2018 ta hanyar amfani da jiragen sama. Hukumar Kula da Filayen Jiragen Saman Turkiyya (DHMI) ta fitar da alkalumanta na watanni 10 na farkon bana. Hakan ya nuna jirage dubu 75 da 583 ne suka tashi tare da sauka a filayen jragen saman Turkiyya a a bangaren kasashen waje inda a safarar cikin gida kuma jirage dubu 61 da 332 suka tashi da sauka.Labarai masu alaka