Kalin: Taimakawa PYD, taimakawa PKK ne

Kakakin Shugaban Kasar Turkiyya Ibrahim Kalin ya bayyana cewar duk wani irin taimako da za a ba wa PYD daidai yake da taimakawa 'yan ta'addar aware na PKK, kuma Turkiyya ba rarrabe 'yan ta'addar da nagari da bata gari.

Bayana taron Majalisar Ministocin Turkiyya Kalin ya sanar da manema labarai cewa, duk taimakon da za a ba wa PYD da YPG kai tsaye ko ta wata hanya daidai da taimakawa 'yan ta'addar aware na PKK, kuma Turkiyya ba rarrabe 'yan ta'addar da nagari da bata gari.

Kakakin Shugaban na Turkiyya ya kara da cewa, daga yanzu dukkan hukumomin Turkiyya za su ci gaba da yaki da ta'addanci ba kakkautawa, kum bukatarsu ga Amurka ita ce ta yanke hulda da PYD da YPG.

Wakilin Amurkana musamman kan Siriya James jeffrey ya bayyana cewar ba sa kallon reshen 'yan ta'addar PKK dake Siriya PYD da YPG a matsayin 'yan ta'adda. Jeffrey ya kuma ce, suna da damuwa game da alakar Turkiyya da PYD da YPG.Labarai masu alaka