Turkiyya: Kakaba wa Iran takunkumi,siyasa ce

Kakakin shugaban kasar Turkiyya,Ibrahim Kalın ya ce,kakaba wa Iran takunkumai da Amurka ta yi, ba komai ba ne face tsantsar siyasa.

Turkiyya: Kakaba wa Iran takunkumi,siyasa ce

Kakakin shugaban kasar Turkiyya,Ibrahim Kalın ya ce,kakaba wa Iran takunkumai da Amurka ta yi, ba komai ba ne face tsantsar siyasa.

Kalın ya yi wannan furucin a wata tashar talabijin mai zaman kanta ta kasar Turkiyya,inda ya ce,

"Amurka na bin son ranta don kakaba wa wannan ko kuma wancan kasar takunkumi.Amma ta san da cewa,sai da aka kashe tsohuwa kan daddawarta,don ba zamu taba yin watsi da maunfofinmu ba.Muna goyon bayan yarjejeniyar nukuliyar Iran,saboda matakin da Amurka ta dauka na saka wa kasar Farisa takunkumai, ba komai ba ne face tsagwaron siyasa".

Amurka ta janye daga yarjejeniyar nukiliyar da ta kulla da Iran a shekarar 2015,inda ta yanke shawarar kakaba wa gwamantin Tahran sabbin takunkumai a ranar 7 ga watan Agustan bana tare da kuma tsananta su a 5 ga watan Nuwamban shekarar 2018.

 Labarai masu alaka