Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 07.11.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 07.11.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 07.11.2018

Babban labarin jaridar Yeni Safak na cewa, a jawabin da Shugaba Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi a wajen taron jam'iyyarsa ta AKP da aka gudanar a zauren Majalisar Dokoki ya ce, takunkumin da Amurka ta saka wa Iran ba ya bisa ka'ida. Ya ce, wannan mataki ne da zai lalata daidaiton duniya. Turkiyya ba za ta yi aiki da wannan mataki na Amurka ba. Hakan ya saba wa kasa da kasa da dokokinsu. A madadin takunkumin za a iya zama a teburin sulhu.

Babban labarin jaridar Hurriyet na cewa, Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya tattauna da 'yan jarida a Cibiyar 'Yan Jaridu ta Kasa dake Tokyo tare da amsa tambayoyinsu. Da yake tabo takunkumin da Amurka ta saka wa Iran Cavusoglu ya ce, hukunta Iran ta wannan hanya zalunci ne ga al'umarta. Turkiyya na dawa da wannan mataki kuma ba za ta yi aiki da shi ba. Ya ce "Ba sa ran za a samu mafita ta wannan hanya."

Babban labarin jaridar Haber Turk na cewa, Ministan Tsaron Turkiyya Hulusi Akar ya ziyar Khartoum Babban Birnin Kasar Sudan. Ya gana da Shugaban Kasar Sudan Umar Al-Bashir da Shugabannin Sojojin Kasar. A yayin ganawar an tabo batun Cibiyar Hporar da Sojoji da Sudan da Turkiyya za su kafa.

Babban labarin jaridar Star na cewa, Turkiyya ta zama kasa dake kan gaba a nahiyar Turai wajen bayar da gudunmowa a harkokin sufurin jiragen sama saboda habakar da ta yi da kaso 8.4 cikin dari a tsakanin 1 ga Afrilu da 30 ga Satumba. Sanarwar da aka fitar daga Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Saman Farar Hula ta ce, Turkiyya ta zama na daya a jerin kasashen Tıurai wajen bayar da gudunmowa a wannan bangaren.Labarai masu alaka