Erdoğan: Ba mu ba kabilanci

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya yi kakkausar suka akan nuna kabilanci a cikin kasa, yayi wannan sukar ne a lokacin da ya kai ziyara a garin Diyarbakir dake a kudu maso gabashin kasar.

A yayinda yake jawabi gabanin bude sabuwar filin wasan kwallon garin Diyarbakir ya jaddada cewa duk wanda ya ce zai nuna kabilanci a cikin kasa zai gamu da fushinmu.

A dayan barayin kuma, Erdogan ya bayyana cewar babu yadda za’a yi a taimakawa wadanda ke zalunta da cin amanar kasa.

Ya bayyana cewa kungiyar ta’addar FETO da DEASH dama PKK dan juma ne da dan jumai.

Ya kara da cewa zamu ci gaba da yin ayyuka tukuru domin gina lardin Diyarbakir da sauran yankunan kasar baki daya.

AALabarai masu alaka