Shugaba Erdoğan ya gana da sarkin Saudiyya

Shugaba Recep Tayyip Erdoğan ya gana da sarkin Saudiyya Salman Bin Abdul-Aziz kan batun Kashoggi.

Shugaba Erdoğan ya gana da sarkin Saudiyya

Shugaba Recep Tayyip Erdoğan ya gana da sarkin Saudiyya Salman Bin Abdul-Aziz kan batun Kashoggi.

A cewar bayanan da aka samu daga fadar shugabancin kasar Turkiyya,a ganawar da suka yi ta wayar tarho a jiya da yamma, shugabannin sun tattauna kan batun dan jarida Kashoggi.

Erdoğan da Salman,sun nuna bukatarsu ta yin aikin cude-ni-in-cude-kan wannan lamarin da ya girgiza duniya,wanda a yanzu haka suke ci gaba da zurfafa bincike a kansa.

Saudiyya da Turkiyya  sun yi amanna kan bai wa junansu labari game da cigaban binciken.

A ranar Lahadin da ya wuce ma, Shugaba Erdoğan ya gana da sarki Salman kan batun na Kashoggi.

 Labarai masu alaka