Dakarun Turkiyya sun kashe 'yan ta'adda 25

A cikin mako gudan da ya gabata dakarun Turkiyya sun kashe 'yan ta'addar PKK 25 a farmakai daban-daban da suka kai musu.

Dakarun Turkiyya sun kashe 'yan ta'adda 25

A cikin mako gudan da ya gabata dakarun Turkiyya sun kashe 'yan ta'addar PKK 25 a farmakai daban-daban da suka kai musu.

Sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta fitar ta ce, a tsakanin 8 da 15 ga Oktoba dakarun Turkiyya sun kaddamar da hare-hare da dama a cikin kasar inda aka kassara 'yan ta'adda 25 

Haka zalika an kama 'yan ta'addar PKK 300, 'yan ta'addar Fethullah FETO 466, na Daesh 53 da kuma wasu mutane 29 a farmakan da aka kai a mako gudan da ya gabata.

Jami'an tsaron Turkiyya sun kuma gudanar da bincike game da shafukan sada zumunta 299 wadanda suka yi farfagandar 'yan ta'adda.

An kuma fara yunkurin gurfanar da mutane 176 a gaban kotu.

A bangaren yaki da gudun hijira ba bisa ka'ida ba kuma an kama bakin haure dubu 7,276.

Tag: PKK , Turkiyya , Hari

Labarai masu alaka