Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 11.09.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 11.09.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 11.09.2018

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, Turkiyya ta bukaci Girka ta kawo karshen mummunar halayyar da ake nuna wa Malaman da aka tura wa Turkawa kuma Musulman Yammacin Trakya marasa rinjaye. Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Hami Aksoy ya ce, an bayyana musu irin damuwar da Turkawa Musulman Yammacin Trakya marasa rinjaye suke da ita. Ya ce, suna kira da a kawo karshen wannan mummunar dabi'a da ake nuna wa Musulmai Turkawa marasa rinjaye na Yammacin Trakya kuma a gyare-gyare da za a yi za a yi su ta hanyar biyan bukatar jama'ar yankin. 

Babban labarin jaridar Hurriyet na cewa, a watanni 3 na 2 na shekarar 2018 tattalin arzikin Turkiyya ya habaka da kaso 5.22. Kungiyar Hadin Kai da Cigaban Tattalin Arziki ta OECD ta ce, Turkiyya ta bar dukkan kasashe mambobinta a baya inda ta zama na 2 a tsakanin kasashe mambobin Tarayyar Turai wajen habaka. A bangaren samar da kayayyaki da kudaden shiga kuma a watanni 3 na 2 na wannan shekarar an samu karin kaso 20.4 sama da na shekarar da ta gabata. Adadin kudin na wannan lokaci ya kama Lira biliyan 884 da miliyan 4 da dubu 260.

Babban labarin jaridar Haber Turk na cewa, Ministan Baitulmali da Kudi na Turkiyya Berat Albayrak ya fitar da sanarwa gme da habakar tattalin arzikin kasarsa. Albayrak ya ce, a watanni 3 na 2 na bana tattalin arzikin Turkiyya ya nuna ya fara daidaituwa. Ministan ya yi kira da a yaki tashin kayan masarufi.

Babban labarin jaridar Yeni Safak na cewa, Turkiyya ta fitar da bushasshen inibi mara kwallo zuwa kasashen waje a tsakanin 2017 da 2018 har tan dubu 279,343 wanda ya kama dala miliyan 452 da dubu 498 An samu habakar kaso 8 na fitar da busasshen inibin. A kasashen gabas mai nisa an samu kari daga kaso 8 zuwa 11 na inibin mara kwallo da ake kai musu daga Turkiyya.

Babban labarin jaridar Star na cewa, a aiyukan haka da ake yi a Kalehoyuk mai tarihin shekaru dubu 5 da ke Kirsehir, an ciro wasu murahu da suke da shekaru 800 wanda aka yi amfani da su a zamanin daular Selcuk. A shekarar 2009 aka fara aiyukan haka a yankin inda daga bisani aka dakata. An sake dawo da aiyukan hakar a shekarar 2012.Labarai masu alaka