Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 10.09.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 10.09.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 10.09.2018

Babban labarin jaridar Hurriyet na cewa, q gundumar Gevas ta lardin Van da ke Turkiyya kuma a Majami'ar Akdamar maş sunan tsaunin an gudanar da bikin da ba a yi shi ba tun bayan shekaru 3. Ministan Raya Al'adu da Yawon Bude Ido Mehmet Nuri Ersoyya bi diddigin bikin na Kiristocin Armeniya wanda wakilin Patrick da ke Turkiyya Başepiskopos Aram Ateşyan d jama'arsa da suka hada da Episkopos Sahak Maşalyan da mataimakin Patrick Janar Mağakya Beskisizyan. Daruruwan mutane daga ciki da wajen Turkiyya ne suka halarci taron.

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, Mai dakin Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, Emine Erdogan ta samu kambin girmamawa na Kungiyar Yabawa Taimakon Dan Adam sakamakon yadda ta dinga nuna damuwa ga Musulman Myammar da ma sauran mutane da ake zalunta a duniya baki daya. A ranar 11 ga watan Satumba za a ba wa Emine Erdogan kyautar a Landan Babban Birnin Birtaniya.

Babban labarin jaridar Haber Turk na cewa, Ofishin Kula da Raya Al'adu da Yawon Bude Ido na Antalya ya sanar da adadin masu yawon bude ido da suka shiga garin ta filiayen tashi da saukar jiragen sama. A wannan shekarar an kafa tarihi a Antalya a bangaren yawon bude ido inda 'yan kasar waje da suka shiga garin suka kai mutum miliyan 9 da dubu 666 da 859.

Babban labarin jaridar Star na cewa, sakamakon aikin madatsar ruwa ta Ilisu da ake ci gaba da yi a gundumar Hasankeyf ta lardin Batman ana kokarin kubutar da kayan tarihi wanda a wannan rana za a sauya wa Hubbaren Imam Abdullahi waje.

 Labarai masu alaka