Ya dau surukinsa kan kafada don taya shi sauke farali

Wani dan kasar Turkiyya mai suna Murat Erbay ya goyi surukinsa,mai shekaru 90 da haifuwa kan kafada,inda ya dinka dawafi da shi tsawon kwanaki 34 da aka yi ana sauke farali a kasa mai tsarki.

Erbay wanda haifaffen yankin Trapzon ne na kasar Turkiyya, ya je aiki hajjin bana tare da maidakinsa, mahaifiyarsa Emine Erbay mai shekaru 76 da haifuwa da kuma surukinsa Ali Kol.

Da yake dattijan biyu na fama da matsalolin dama,wadanda ke da nasaba da tsufa da kuma rashin lafiya,sai ya siya wa gyatumarsa gujerar guragu da nufin matarsa ta dinka tuka ta, yayin shi kuma, ya yanke shawarar daukar surukinsa kan kafada.

Ko a lokacin da 'yan jaridun suka tarbi alhazzan Turkiyya a filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Trapzon,an ga Murat dauke surukinsa.Labarai masu alaka