Kashin 'yan ta'adda na ci gaba da bushewa

A makon da ya gabata,sojojin Turkiyya sun yi nasarar tisa keyar ‘yan ta’addar PKK da na Daesh 62 barzahu,wadanda a ciki har da wasu manyan kusoshi 4.

Kashin 'yan ta'adda na ci gaba da bushewa

A makon da ya gabata,sojojin Turkiyya sun yi nasarar tisa keyar ‘yan ta’addar PKK da na Daesh 62 barzahu,wadanda a ciki har da wasu manyan kusoshi 4.

Sojojin Turkiyya na ci gaba da namijin kokarin wajen ganin sun samar da zaman lafiya a ciki da wajen kasar, ta hanyar fatattakar ‘yan kungiyoyin ta’addar PKK/KCK/PYD-YPG da na Daesh.

Tun ranar 31 ga watan Agustan shekarar 2018 ya zuwa yau,sojojin ke ci gaba da yin luguden wuta kan ‘yan ta’addar PKK a yankunan Şirnak,Siirt,Hakkari,Diyarbakir da Mardin na Turkiyya da kuma arewacin Iraki,babbu kakkautawa.

A wadannan farmakan,an kashe ‘yan ta’adda 22 a Turkiyya 44 kuma, a Iraki,tare da lalata bindigogi da kuma bama-bamai masu dumbin yawa.Labarai masu alaka