Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 07.09.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 07.09.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 07.09.2018

Babban labarin jaridar Yeni Safak na cewa, Kamfanunnukan samar da kayan tsaro da ke da alaka da Asusun Karfafawa Dakarun Turkiyya sun kara kuzari da karko sama da shekarar da ta gabata inda suka samu riba a bana ta dala biliyan 10.5. Kayan da ake samarwa masu inganci a tsaro kuma ake fitar da su kasashen waje na ara habaka bangaren masana'antun tsaro da ma kamfanunnukan Turkiyya baki daya. Masana'antun kayan tsaro na Turkiyya na jerin guda 100 da ake da su a duniya.

Babban labarin jaridar Hurriyet na cewa, a gundumar Ibadi da ke Antalya da ake da kogon da ya ke da korama a cikinsa masu yawon bude ido na cigaba da kwarara. A kowanne yanayi 'yan yawon bude ido na shiga kogon Altinbesik. Kogin na da dandanon soda da kalar shudi mai haske. Kogon na a tudu mai tsayin mita 450 daga teku kuma ana shigar sa da kanana jiragennruwa.

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, a watanni 7 na farkon wannan shekarar adadin Jamusawa da suka ziyarci Turkiyya ya karu da kaso 20 widan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata wanda ya kama mutane miliyan 2 da dubu 321. Daya daga cikin kamfanunnukan Jamus masu bincike na Trevo Trend, ta bakin Darakta Janar dinsa Matthias Lange ya sanar da cewa, Turkiyya kasa ce mai jan hankali, a cikin kankanin lokaci ana ta bayyana bukatar zuwa kasar daga Jamus. 

Babban labarin jaridar Star na cewa, a tsakanin 20 da 23 ga watan Satumba za a gudanar da bikin kayan jiragen sama na Teknofest a Istanbul. Za a gudanar da bikin a filin tashi da saukarjiragen sama na birnin. Za a baje-kolin jiragen sama, jiragemarasa matuki, mutum-mutumin Fetih 1453. Akwai nau'ikan jiragen sama marasa matuki har guda 12 da za a baje kolinsu.

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, adadin fasinjoji da aka dauka a filayen tashi da saukar jiragen sama da ke Turkiyya sun karu a bana d kaso 4.8 wanda suka kama mutum miliyan 22.8. Fasinjojin kasashen waje da aka dauka kuma a tsakanin watan Janairu da Agustan bana ya karu da kaso 10.8 wanda ya kai mutane miliyan 143.2.Labarai masu alaka