Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 10.08.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 10.08.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 10.08.2018

Babban labarin jaridar Haber Turk na cewa, Mai Ba Wa Majalisar Dinkin Duniya Shawara Kan kasar Siriya Jan Egelang ya bayyana cewa, miliyoyin fararen hula da ke garin Idlib na fuskantar barazana. Ya ce, domin hana afkuwar wani rikici a Idlib Turkiyya, Iran da Rasha za su hada kai. Ya ce, idan ta kama za a yi kira ga Turkiyya da gwamnatin Ankara kan su bude iyakokinsu ga 'yan gudun hijirar da za su bar yankunan.

Babban labarin jaridar Hurriyet na cewa, An sanar da ranar da jirgin farko zai tashi a sabon filin tashi da saukar jiragen sama da ake gina wa a Istanbul. An kuma sanar da ina ne jirgin zai je. Jirgin zai tashi daga Istanbul zuwa Jamhuriyar Arewacin Cyprus Bangaren Turkiyya da kuma Azerbaijan. A ranar 29 ga watan Oktoba za a fara aiki sosai a filin wanda aka kammala aikinsa da kaso 95. A ranar 31 ga Oktoba a Ankara kuma za a gudanar da babban biki da misalin karfe 14:00. 

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, Shafin Wayar da Kan Jama'a na Kamfanin Jiragen Saman Turkiyya Turkish Airlines ya bayyana adadin fasijojin da suka dauka a tsakanin watan janairun da Yulin 2018. An bayyana cewa, a watanni 7 na farkon 2017 an yi jigilar fasinjoji miliyan 37.5 inda a shekarar 2018 kuma aka yi jigilar miliyan 43.2 wanda hakan ke nuna an samu karin kaso 15.2. Asafarar cikin gida an samu kari da kaso 17 inda a safarar kasashen waje kuma aka samu da kaso 13.8. Cikar cirage kuma ya samu karinmaki 3.8 inda ya zama kaso 81.2.

Babban labarin jaridar Yeni Safak na cewa, A gundumar Dargecit da ke lardin Mardin na Turkiyya a yayin gudanar da haka da fadada kogin Ilisu da ke filin Bocuklu an samu wasu abubuwan wuya da suke da shekaru dubu 8,200. Sarkokin guda 2 ne daya na mace daya na namiji inda aka kai su gidan ajje kayan tarihi.Labarai masu alaka