Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 09.08.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 09.08.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya  09.08.2018

Babban labarin jaridar Yeni Şafak na cewa ministocin shari'a da harkokin cikin gidan ƙasashen Turkiyya da Amurka sun zauna domin warware rikicin Andrew Craig Brunson. A zaman farko da aka yi a birnin Washington mataimakin ministan harkokin wajen Turkiyya Sedat Önal tare da tawagar mutane tara suka halarta.

Babban labarin jaridar Hurriyet na cewa a halin yanzu an samu ƙaruwar fitar da ƙarafa daga ƙasar Turkiyya da kaso 26.7 cikin ɗari da zunzurutun kudi dala biliyan 8.4 idan aka kwatanta da na watanni 7 shekarar 2017. Ƙasashen nahiyar Turai ne Turkiyyar tafi fitar da ƙarafa zuwa garesu. A inda aka samu ƙaruwar fitar ƙarafan da kaso 62.9 da kudi dala biliyan 3 da miliyan 604 da dubu 730 idan aka kwatanta da na watanni 7 a shekarar 2017

Babban labarin jaridar Sabah na cewa ministan makamashin kasar Turkiyya Fatih Donmez ya bayyana cewar bayan kammala cibiyar nukiliyar Akkuyu da Sinop za'a kaddamar da na uku a Trakya wanda zaa gudanar da haɗin gwiwar kasar China.

Babban labarin jaridar Vatan na cewa ministan sufurin ƙasar Turkiyya Mehmet Cahit Turhan ya bayyana cewar ƙasar ta shirya wa mihimman aiyukan da za ta gudanar. Kataɓaren aikin mai taken "Mega Project" zai kasance hanyar karkashin kasa mai hawa uku a lstanbul zai kasance na farko a duniya.

Babban labarin jaridar Star na cewa masallacin garin Kastamonu na katako da aka yi a shekarar 1366 ba tare da amfani da ƙusa ba na ci gaba da jan hankalin mutane. Masallacin da dan Adil Bey mai suna Emir Mahmut da ake kira da sunan Masallacin Emir Mahmut na ya yi na ci gaba da burge ƴan yawon buɗe ido. Masallacin dake cikin littafin tarihin UNESCO na wuccin gadi, ana ci gaba da yunƙurin sanya shi cikin littafi na din-din-din.Labarai masu alaka