Jirgin 'yan gudun hijira ya kife a Turkiyya

Jami'an tsaron tekun sun je wajen bayan samun labarin kifewar jirgin ruwan 'yan gudun hijirar a yankin.

Jirgin 'yan gudun hijira ya kife a Turkiyya

Jami'an tsaron tekun sun je wajen bayan samun labarin kifewar jirgin ruwan 'yan gudun hijirar a yankin.

An kuma aike da motocin daukar marasa lafiya da dama zuwa yankin.

Rahotanni da aka fara samun sun ce, jirgin ruwan na dauke da 'yan gudun hijira 13 da suke kokarin barin Turkiyya ba bisa ka'ida ba inda mutane 9 da suka hada da yara kanana suka mutu.

An kubutar da mutane 4 a lamarin.

Jami'an tsaron ruwa na ci gaba da aiyukan ceto a yankin.Labarai masu alaka