Erdoğan: Ronaldo ne gwanina ba Messi ba

Shugaba Erdoğan ya jinjina wa Ronaldo kan goyon bayan Falasdinawa da Musulman Arakan da kuma bajintarsa a gasar cin kofin duniya ta bana.

Erdoğan: Ronaldo ne gwanina ba Messi ba

Shugaba Erdoğan ya jinjina wa Ronaldo kan goyon bayan Falasdinawa da Musulman Arakan da kuma bajintarsa a gasar cin kofin duniya ta bana.

Erdoğan ya yaba wa dan wasan na kasar Portugal a wani taro mai taken "Haduwar matasa da Fasaha" wanda Hukumar fasahar kere-keren jiragen sama ta Turkiyya ta shirya, da zummar amsa tambayoyin matasan kasar, gabanin zabukan ranar 24 ga watan Yunin bana.

Da aka tambayi shugaban na Turkiyya game dan wasan da ya fi so tsakanin Messi da Ronaldo,sai Erdoğan ya ce,

"Na fi son Ronaldo.Shi ne gwanina.A gaskiya babban dan wasa ne da ya kamata a yabawa,Ina matukar son sa sabili da goyon bayan da yake yi wa Falasdinawa da Musulman Arakan.Ina jinjina masa".Labarai masu alaka