Sojojin Turkiyya na ci gaba da tsaftace Afrin daga PKK

Sojojin Turkiyya na ci gaba da tsaftace Afrin daga kungiyar ta'adda ta PKK da sauran haramtattun da suka yi kaka gida a Siriya da kuma kan iyakokinta.

Sojojin Turkiyya na ci gaba da tsaftace Afrin daga PKK

Sojojin Turkiyya na ci gaba da tsaftace Afrin daga kungiyar ta'adda ta PKK da sauran haramtattun haramtattun kungiyoyin da suka yi kaka gida a wannan kasar da kuma kan iyakokinta.

Tun a lokacin da aka fara kaddamar da farmakan Reshen Zaitun ya zuwa yau, sojin na Turkiyya sun kwace iko da Afrin da Jerabulus ta hanyar fatattakar 'yan PKK da DAESH.

Abinda yasa Siriyawa ke ci gaba da komawa gida a wadannan yankunan da aka kwato daga hannun azzaluman kungiyoyin.

Hukumomin kasar Turkiyya sun tabbatar da cewa, kusan 'yan kasar Sham dubu 200 ne suka koma gida. 

A na hasashen ninkuwar yawan masu neman mafakan da zasu koma kasarsu ta ainahi,ganin yadda kwanciyar hankali da lumana suka dawo a yankunan da a baya, suka kasance tamkar "Jahannama" ga al'umar kasar ta Siriya.

 


Tag: sham , turkiyya

Labarai masu alaka