'Siriyawa sun fara komawa gida bayan mu tsaftace Afrin daga 'yan ta'adda'

Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdoğan ya ce sun ragargaje kungiyoyin ta'addar da ke boye a bishiyoyin Sham.

'Siriyawa sun fara komawa gida bayan mu tsaftace Afrin daga 'yan ta'adda'

Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdoğan ya ce sun ragargaje kungiyoyin ta'addar da ke boye a bishiyoyin Sham.

Erdoğan ya furta wannan kalamin a zauren baja koli na fadar shugabancin Turkiyya yayin wani sahur da yayi da magadan garuruwan yankunan kasarsa.

Shugaban na Turkiyya ya ce,

"Mun ragargaje kungiyoyin da ke boye a bishiyoyin Sham.A Judi,Gabar,Tendürk da Bestler Deresi na Turkiyya mun yi galaba kan 'yan haramtattun kungiyoyin"

Shugaba Erdoğan wanda ya tunatar da farmakan da aka kaddamar kan kungiyoyin ta'adda a Siriya ya ce,

"A kowane bangare mun tsaftace akalla wani yanki mai fadin kilomita dubu 4,a yanzu Siriyawan da suka nemi mafaka a kasarmu na ci gaba da komawa gida.Kusan masu neman mafaka dubu 200 sun koma kasarsu ta ainahi.Muna fata yawansu zai dada karuwa".Labarai masu alaka