"Idan wadanda ke mutuwa Musulmai ne, sai kowa yayi shiru ya zuba na mujiya"

Kakakin shugaban Turkiyya,Ibrahim Kalın yayi Allah wadai da yadda duniya ta zuba ido tana kallon zaluncin da Isra'ila take ci gaba da yi wa Falasdinawa tsawon shekaru 70, ba tare da ta dauki matakan taka ma ta birki ba.

"Idan wadanda ke mutuwa Musulmai ne, sai kowa yayi shiru ya zuba na mujiya"

Kakakin shugaban Turkiyya,Ibrahim Kalın yayi Allah wadai da yadda duniya ta zuba ido tana kallon zaluncin da Isra'ila take ci gaba da yi wa Falasdinawa tsawon shekaru 70, ba tare da ta dauki matakan taka ma ta birki ba.

Kalin yayi cikakken bayani a wata tashar rediyo mai zaman kanta na Turkiyya.

Kakakin ya sake waiwayar kisan gillar da Isra'ila ta yiwa Falasdinawa,wadanda ke gwagwarmayar hana Amurka maida ofishin jakadancinta daga Tel Aviv zuwa Qudus,inda ya ce,

"A batun Qudus,akwai babbar cuzgunawa,babban rashin adalcin da aka share shekaru 70 ana yinsa.A hakikannin gaskiya, duniya ta shaida hakan.Muna ci gaba da ganin sabbin fuskokin wannan matsalar daki-daki.Kisan da aka yi a ranar 14 ga watan Mayu,an rubuta shi a shafukan tarihi a matsayin 'Bakar Litinin' ".

Kalin ya sanar da cewa,maida ofishinj jakdancin Amurka zuwa Qudus,babban kuskure ne wanda babu kamar sa a duk tarihin duniya,haka zalika,

"Daga yau, gwamnatin Amurka ta Donald Trump,ta fadi a yunkurinta ta warware mastalolin Gabas ta Tsakiya, musamman ma abinda ya jibanci magance rikicin Falasdinawa, a fannin siyasa da kuma sanin-yakamata.Daga yau, Amurka ba za ta taba kasancewa mai shiga tsakani marar nuna fifiko ba, a batun samar da kasashe biyu,watau Isra'ila da Falasdinu.Tuni Falasdinawa suka fara tsokaci kan wannan lamarin,inda suka ce basu yi wa Amurkawa kallon masu-shiga tsakani,haka zalika basu kaunar ganin su" inji Ibrahin Kalın.

Bugu da kari, wagmatin Amurka ta ce ta share watanni da dama tana kokarin samar da sabon tsarin samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin Gabas ta Tsakiya,Kalın ya ce,amma idan duniya ta nemi su bayyana aniyarsu,sai su ki.

Kalın ya ce a ranar 14 ga watan Mayun,lamurra 2 ne suka faru a lokaci daya, a maduban akwatinan talabijojin duniya,yayin da a gefe daya Amurka ke murna a daya bangare kuma,hıtunan gawarwakin Falasdinawa ke kwance kan iyakar zirin Gaza,kana,

"Wadannan hotunan, ababen kunya ne.Kunyar da aka rubuta a tarihi Isra'ila.Kunyar da aka rubuta a tarihin Amurka.Wannan babban kaskanci ne"

Kalin ya sanar da cewa,sheakru 3 kenan da shuagabn kasar Turkiyya,Recep Tayyip ke jan akalar kungiyar kasashen Musulmai ta OIC,inda a tsawon wannan lokacin ya shirya tarukan koli da dama, kan batun Qudus,haka zalika,

"A gaskiya,Shugaba Recep Tayyip Erdoğan ya kasance masoyin Qudus mafi girma.Jagora ne wanda zuciyarsa ke bugawa don Qudus.Shi yasa ya ke ci gaba da aiki dare da rana".

Daga bisani kakakin na Erdoğan, ya bayyana irin muhimmanci da kare manyan wuraren addini da na tarihin Islama da ke Qudus ke da su,inda ya ce

"Idan muka saki muka yi shakka ko kuma yarda da daya daga cikin sharuddan Isra'ila daidai kwayar zarra,to ku sani cewa,babu makawa nan da shekaru 20 zuwa 30 masu zuwa Qudus da masallacin al Aqsa,zasu gushe daga doron duniya.Shi yasa dole ne, mu yi taka-tsantsan".

Ibrahim Kalın ya ce batun aika bataliyar sojoji zuwa Qudus don tabbatar da zaman lafiya da kuma kare Falasdinawa,abu ne mai matukar muhimmanci,saboda,

"Idan muka dubi Falasdinawa,sai mu gane cewa basu da komai.Basu da runduna,bbasu da 'yan sanda, basu da makamai,sojoji,duk da suna fuskantar daya daga azzaluman sojoji na Gabas ta Tsakiya.Sojojin Isra'ila sun mallaki makaman kirar Amurka,makaman kare dangi da bama-baman nulikiya.An kashe dubban Falasdinawa tun shekarar 1947,an kashe wasu karin daruruwa a watannin da suka shude,inda dubbai suka jikkata,wasu dubbai kuma an garkame su.Idan abinda ya faru da Falasdinawa ya afku a wani bangare na duniya, da tuni an aika sojoji don kiyaye zaman lafiya.Amma da yake Musulami ne ke mutuwa,sai kowa yayi shiru ya zuba na mujiya".Labarai masu alaka