Shugaba Erdoğan ya gana da mai martaba sarki Salman

Shugaban kasar Turkiyya,Recep Tayyip Erdoğan ya gana ta wayar tarho da mai martaba sarki Salman bin Albdulaziz na Saudiyya.

Shugaba Erdoğan ya gana da mai martaba sarki Salman

Shugaban kasar Turkiyya,Recep Tayyip Erdoğan ya gana ta wayar tarho da mai martaba sarki Salman bin Albdulaziz na Saudiyya.

A cewar bayanan da aka samu daga fadar shugabancin Turkiyya,Wrdoağn da Salman sun tattauna kan lamurran da ke ci gaba da wakana a yanzu haka a Falasdinu.

Shugabbanin 2 sun jadadda cewa,lokaci ya zo da ya kamata Musulmai su hada karfi da karfe don kalubalantar Isra'ila wacce ta kashe Falasdinawa 62 kan iyakar zirin Gaza,haka zalika sun  yi musayar yawu game da taron gaggauwa da kungiyar kasashen Musulmai za ta yi a ranar Jumma'ar nan mai zuwa a birnin Santambul na Turkiyya.

A 'yan kwanakin nan shugaba Erdoğan ya gana da sarkin Kuweit Sheikh Sabah al-Ahmed al-Jabir as Sabah,takwaransa na Falasdinu Mahmut Abbas,sarkin Jordan Abdallah na II, da kuma firaministan Malaysia Mahathir Muhammad don warware bakin zaren rikicin Qudus.Labarai masu alaka