Manyan labren wasu jaridun Turkiyya 17.05.2018

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan akan lamurkan dake afkuwa a Falasdinu  ya gana da shugaban Jamus; Angela  Merkel, Iran; Hasan Ruhani, Rasha; Vladimir Putin  daya bayan daya ta wayar tarho.

Manyan labren wasu jaridun Turkiyya 17.05.2018

Manyan labren daga wasu jaridun Turkiyya 17.05.2018

Babban labarin jaridar Sabah na cewa shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan akan lamurkan dake afkuwa a Falasdinu  ya gana da shugaban Jamus; Angela  Merkel, Iran; Hasan Ruhani, Rasha; Vladimir Putin  daya bayan daya ta wayar tarho. a yayinda shugaba EWrdoğan ke ganawa da shugaban Jamus sun tabo batun rigimar dake afkuwa a Gaza dake muzgunawa Falasdinawa, a yinda suka aminta akan daukar kwararan matakai domin warware matsalar baki daya. Haka kuma Erdoğan ya gana da Ruhani akan lamarin daga karshe kuma ya tattauna da Putin akan matsalolin kasar ta Falasdinu.   

Babban labarin jaridar Star na cewa Ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Mevlüt Çağuşoğlu zai gana da takwaransa na Amurka Mike Pompeo a ranar 4 ga watan Yuni. A ganawar da zasu yi a babban birnin Amurka, Washington zasu tattauna akan lamurkan kasar Siriya, gabas ta tsakiya, dangantakar kasashen biyu, da kuma lamaurkan kalubalantar kungiyoyin ta'addanci PKK da FETO/PDY.

Babban jaridar Vatan na cewa hafsan sojojin kasar Turkiyya Hulusi Akar a yayinda yake halartar taron kungiyar NATO a Brussels ya gana da takwarorinsa na Girka da Amurka. A inda suka fara tattunawa akan lamurkan tsaron yankin Medeterranian da takwaransa na Girka daga bisani kuma ya gana da na Amurka Joseph Dunford inda suka tattauna akan lamurkan Siriya da gabas ta tsakiya.

Mataimakin Firaministan Turkiyya mai kula da tattalin arziki Mehmet Şimşek ya yada a shafinsa na twitter da cewar laömurkan hadahadar canji zasu dai-daita bayan an kammala zabe, labari da wakilin kafar yada labaren Bloomberg Nwes ta Turkiyya dake shashen canji Benjamin Harvey ya rawaito na nuni da cewa lamurkan hadahadar canji zasu inganta bayan an kamala zabe a kasar.

Babban labarin Yeni Şafak na cewa daya daga cikin mataimakan firaministan Turkiyya Recep Akdağ ya kai ziyara a Jamhuriyar Demokradiyyar Cyprus reshen Turkiyya a inda ya gana da shugaban kasar Mustafa akıncı da kuma firaministan kasar Tufan Erhürman daya bayan daya. Da yake jawabi ya yi sharhi akan lamurkan Falasdinu a inda ya bayyana cewar Turkiyya nada bukatar ta dauko wadanda suka sami raunuka daga Falasdin amma yin hakan na bukatar saukar jirginta a Isra'ila ko kuma Misira lamarin da dukkanin kasashen biyu basu amince dashi ba.

 Labarai masu alaka