Dubun shahararren dan ta'adda Burhanli ta cika
Rundunan sojan Turkiyya ta bayyana cewar ta yi nasarar kashe dan ta'addar da take nema ruwa a jallo mai suna Birdal Burhanlı a yankin arewacin Iraqi.

Rundunan sojan Turkiyya ta bayyana cewar ta yi nasarar kashe dan ta'addar da take nema ruwa a jallo mai suna Birdal Burhanlı a yankin arewacin Iraqi.
Kamar yadda rundunar sojan ta sanar a ranar 21 ga watan Maris ta yi nasarar kashe shahararen dan ta'addar da take nema mai suna Birdal Burhanlı wanda akawa lakabi da "Agiri Mazlum Pirdoğan" a yankin Hakurk-Kani Rash dake arewacin Iraqi.
Burhanlı ya kasance wanda ke jagorantar ta'addanci a yankin Hakurk.