• Bidiyo

An gano jikkunan 'yan mata 8 daga cikin 11 da suka mutu a hatsarin jirgin sama a Iran

An gano jikkunan mata 8 daga cikin 11 da suka yi hatsari a jirgin saman Kamfanin Basharan Holding na Turkiyya wanda ya fado a kudu maso-gabashin Iran.

A sanarwar da Mataimakin Shugaban Kungiyar Bayar da Agaji ta Red Crescent na jihohin Jaharmahal da Bahtiyari, Riza Zahir ya yi ga kamfanin dillancin labarai na Iran ya bayyana cewa, jami'an ceto sun je wajen da lamarin ya faru da misalin karfe 3 na daren Litinin din nan inda suka samu nasarar gano jikkunan mata 8.

Zahiri ya ce, saboda kone wa dagargaje wa ba a iya gane wasu jikkunan mata 2 ba inda ake ci gaba da neman 1.

Daraktan magance Rikici na yankin Kiyar Kademali mardani ya ce, jirgin ya taso daga kasar Hadaddiyar Daular Larabawa zuwa Istanbul inda ya fado a gundumar Kiyar da ke tsakanin jihohin Jaharmahal da Bahtiyari.

Ya ce, dukkan mutane 11 da ke cikin jirgin sun mutu.

A cikin jirgin akwai 'yar dan kasuwa Basharan da kawayenta 7 sannan sai matuka jirgin 2 da mai hidima 1.Labarai masu alaka