Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Star Firaministan Turkiyya Binali Yildirim ya yi taron manema labarai da takwaransa na Makedoniya Zoran Zaev wanda ya ziyarci Ankara. Da ya ke tabobatun hare-haren "Reshen Zaitun" Yildirim ya ce, idan Turkiyya ba ta dauki mataki kan wannan yanki ba, t dukkan Turai ne za su fuskanci matsalar ta'addanci da ta gudun hijira. Kuma abin takaici Tarayyar Turai ba ta daukar wani matakin magance wannan abu.

Babban labarin jaridar Haber Turk na cewa, Mataimakin Firaministan Turkiyya Hakan Çavuşoğlu ya yi wani jawabi kan abubuwan da suke faru wa a duniya a wata hira da ya yi a TRT. Çavuşoğlu ya tabo batun ware dala miliyan 300 da Amurka ta yi a kasafin kudin 2019 don horar da 'yan ta'addar PYD/PKK a Siriya, da kuma dala miliyan 250 don saya musu makamai da kayan yaki inda ya ce, idan Amurkan ta ci gaba da yin wannan abu t alakarta da Turkiyya za ta iya lalacewa baki daya, wanda da ma ai kar ta san kar suke.

Babban labarin jaridar Yeni Şafak na cewa, Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Çavuşoğlu ya yi wasu jawabai masu jan hankali sosai kafin takwaransa na Amurka Rex Tillerson ya ziyarci Turkiyya. Çavuşoğlu ya tunatar da cewa, Amurka ba ta cika alkawarurrukanta. "Ko dai a gyara ko kuma a bata gaba daya."

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, Minisdtan Tsaron Filifin Delfin Lorenzana ya bayyana cewa, suna tunanin sanya hannu da kasashen Turkiyya, Koriya ta Kudu, Rasha da China don sayen jiragen yaki masu saukar ungulu.Labarai masu alaka