Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, Majalisar Ministocin Turkiyya ta yi taro a ranar Litinin din nan karkashin jagorancin shugaban kasar Recep Tayyip Erdoğan. Bayan kammala taron da ya dauki kusan awanni 2, mataimakin Firamminista kuma Kakakin gwamnatin Turkiyya Bekir Bozdağ ya gudanar da taron manema labarai inda ya yi bayani game da abin kunyar da aka yi a yayin atisayen NATO a kasar Norway. Bozadg ya ce "Wannan abu ya shafi mutanen da aka rataya hotunansu. Yadda wasu ma'aikatan NATO suka yi amfani da shafukan Kungiyar don cutar da Turkiyya abu ne na bayar da misali. Ya kamata a sani cewa, Turkiyya mamban NATO ce mai muhimmanci. Kuma za ta ci gaba da bayar da gudunmowa saboda wannan matsayi da ta ke da shi.

Babban labarin jaridar Haber Turk na cewa,Majalisar Dokokin Turkiyya ta zabi sabon shugaba da zai yi jagoranci a hskearun 2 na karshen zango na 26. Majalisar ta yi taro inda a zagayen farko na zaben da aka yi babu wanda ya yi nasara wanda hakan ya sa aka tafi zagaye na 3. A wannan zagaye shugaban majalisar ısma'il Kahraman ne aka sake zaba. Shugaba Recep Tayyip Erdoğan ya taya Kahraman murnar sake zaben sa da aka yi.

Babban labarin jaridar Star na cewa, Ministan makamashi da albarkatun kasa na Turkiyya Berat Albayrak ya ce, za a samar da rubun albarkatun iskar gaz a Hatay da gabar tekun Saros.Albayrak ya yi jawabi a gaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dokokin Turkiyya inda ya kara da cewa, akwai bukatar a magance dogaro kan kasashen waje game da bukatar albarkatun man fetur. Sakamakon haka za su yi duk mai yiwuwa wajen samar da rumbunan adana man.

Babban labarin jaridar Yeni Şafak na cewa, ma'aikatar raya al'adu da yawon bude ido ta kasar ta fara aikin tabbatar da kubutar da al'adun kasar da ke shirin bace wa. Ma'aikatar ta fara aikin tsare wasu kayan al'adu 4. A yanzu an fara aikin kiyaye Bikin Lokacin Bazara, Labarai da Hikayoyin Dede Korkut, Wasan Harba Kwari da Baka da kuma Islık Dili wanda ke bayar gwarzantar Turkawa.Labarai masu alaka