An kama bakin haure 50 a Turkiyya

An kama bakin haure su 50 a gundumar Ayvalık ta lardin Balikesir na Turkiyya a lokacin da suke kokarin barin kasar ta barauniyar hanya.

An kama bakin haure 50 a Turkiyya

An kama bakin haure su 50 a gundumar Ayvalık ta lardin Balikesir na Turkiyya a lokacin da suke kokarin barin kasar ta barauniyar hanya.

Sanarwar da fadar gwamnan Balikesir ta fitar ta ce, wasu jami'an sandan shashen yaki da fataucin mutane ne suka kama mutanen tsibirin Patriça tare da wadanda suka shirya fitar da su zuwa Girka.

Mutanen suna cikin motocin bas kanana 2, da kuma kananan motoci 2.

An fara bincike kan lamarin bayan kama bakin hauren tare da Turkawa 6 da suka shirya fataucinsu.Labarai masu alaka