Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Hurriyet na cewa, a yau ne Mustafa Kamal Ataturk ya cika shekaru 79 da mutuwa. Ana gni tare da amfana da irin abubuwan da ya kafa a lokacin yana raye. Al'umar Turkiyya na nuna so da kauna tare da kewar Ataturk wanda shi ne ya kafa Sabuwar Turkiyya. A ranar 10 ga kowanne watan Nuwamba 'yan kasar a bangarori daban-daban na gudanar da tarukan tuna wa da Ataturk. A wannan rana dubunnan mutane na zuwa Anitkabir inda Kabarin Ataturk ya ke. A sakon da shugaban kasar Turkiyya Recep tayyip Erdoğan ya fitar game da wannan rana ta 10 ga Nuwamba ya ce, Gazi Mustafa Kamal shugaba ne da ake girmama wa wanda ya jogaranci kubutar Turkiyya tare da kafa jumhuriya.

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, Firaministan Turkiyya Binali Yıldırım ya gana da mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence. A lokacin da Yıldırım ya ke tafiya New York daga Washington ya zanta da 'yan jaridu inda ya ce, sun tattauna kan batutuwa da suka shafi alakar Amurka da kuma batutuwan da suka shafi yankunansu. Yildirim ya ce, ana so a gyara alakar kasashen 2. Dole ne a dauki wani babban mataki game da FETO. Sanarwar da aka fitar daga fadar White House ta ce, za a bude sabbin shafuka a alakar kasashen 2.

Babban labarin Yeni Şafak na cewa, Firaministan turkiyya Binali Yildirim a yayin ziyarar da ya ke a Amurka ya gana da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. A sanarwar da Yildirim ya yi game da ganawar da suka yi ya ce, Sakataren ya yaba da irin nauyin 'yan gudun hijira da Turkiyya ta dauka. Ya ce, fatansu shi ne sauran kasashen duniya su karbi wasu 'yan gudun hijirar.

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, An saka hannu kan aikin samar da taurarin dan adam da Turkiyya za ta harba zuwa duniyar wata a shekarun 2020 da 2021. Kamfanin Airbus ne zai samar da taurarun na 5A da 5B wanda Turkiyya kuma za ta jagoranci aikin. An sanya hannu kan yarjejeniyar dala miliyan 500 don gabatar da aikin. Za a harba tauraron 5A a shekarar 2020 sai na 5B a shekarar 2021 ta hanyar amfani da rokar Falcon 9 na kamfanin SpaceX.Labarai masu alaka