Turkiyya zata ƙera tauraron dan adam

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya karɓi baƙwancin tawagar kanfanin Tesla da Space X tare da babban shugaban kanfanin Elon Musk.

Turkiyya zata ƙera tauraron dan adam

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya karɓi baƙwancin tawagar kanfanin Tesla da Space X tare da babban shugaban kanfanin Elon Musk. 

Maimagana da yawun shugaban ƙasar lbrahim Kalın ya bayyana cewar kanfunan zasu yi aiki tare da haddin gwiwa Turkiyya don samar da tauraron dan adam sanfarin Türksat 5A da 5B ga ƙasar Turkiyya. Haka kuma Musk ya bayyana cewar kanfanin sa da Turkiyya zasu yi aiki bai ɗaya don bunkasa lamurkan makamashi.

Kalın ya ƙara da cewa a yau za'a gudanar da wasu yarjejeniyoyin da suka shafi harkar makamashin iskar rana da tauraron dan adam tsakanin kamfanin da Turkiyya. Inda ya kara da cewa hakan zai baiwa Turkiyyar damar samun tauraron dan adam na ƙashin kanta. 

Tuni dai Turkiyya ta soma ɗauka matakan samar da tauraron dan adam sanfarin Türksat 6 wanda zata ƙera da kanta.

 Labarai masu alaka