Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 9.11.2017

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 9.11.2017

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 9.11.2017

Babban labarin jaridar HaberTürk na cewa shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya karɓi baƙwancin tawagar kanfanin Tesla da Space X tare da babban shugaban kanfanin Elon Musk. Mai magana da yawun shugaban ƙasar lbrahim Kalın ya bayyana cewar kanfunan zasu yi aiki tare da haddin gwiwa Turkiyya don samar da tauraron dan adam sanfarin Türksat 5A da 5B ga ƙasar Turkiyya. Haka kuma Musk ya bayyana cewar kanfanin sa da Turkiyya zasu yi aiki bai ɗaya don bunkasa lamurkan makamashi.

Babban labarin jaridar Hürriyet na cewa Firaministan Turkiyya Binali Yıldırım ya gana da shugaban komitin hurɗar ƙasa da ƙasa na majalisar dokokin Amurka Bob Crocker a ziyarar da ya kai, zai kuma gana da mataimakin shugaban ƙasar Mike Pence inda zasu tattauna akan lamurkan tsaro da kuma sulhunta waɗansu lamurkan dake tsakanin ƙasashen

Babban jaridar Sabah na cewa a taron ƙasashen NATO da ake gudanarwa a Belgium ministan tsaron Turkiyya Nurettin Canikli, Shugaban rudunar sojar Faransa Florence Parly da ministan tsaron ltaliya Roberta Pinotti sun rattaɓa hannu akan haddin gwiwa tsaro tsakanin kasashen su. Haka kuma Turkiyya, Faransa da ltaliyar sun amince akan aiki bai ɗaya domin samar da makamashi da ƙirar makaman nukiliya.

Babban labarin jaridar Yeni Şafak na cewa an bayyanar da Majalisar Dokokin hukumar UNESCO a taron ƙolin da ake gudanarwa na 39 a Paris babban birnin Faransa. Daga cikin su harda ƙasar Turkiyya da zasu ja ragamar tafiyar da harkokin hukumar daga 2017-2021, ƙasashe 134 suka kaɗawaTurkiyya  kuri'a a taron.

Babban labarin jaridar Vatan na cewa a yau kungiyar kwallon kafar Turkiyya zata kara da ta Romaniya a garin Cluj dake Romaniya da ƙarfe 21.15. Za'a yi wasan ne a filin wasan Costantin Radulescu wanda alkalin wasa dan Portugal Tiago Bruno Looes Martins da kuma Ricardo Jorge Ferreira Santos da Luis Andre Ferreira Pinto Campos a matsayin mataimaka.Labarai masu alaka