Turkiyya ta gwada harba makami mai linzami kirar kasar

Kwamandan Rundunar Teku ta Turkiyya Manjo Admiral Ahmet Cakir ya bayyana cewa, a karon farko sun gwada harba makami mai linzami kirar Turkiyya inda a shekara mai zuwa za a fara gwada harba shi a kan jiragen yaki da ke kan teku.

Cakir ya yi jawabi a wajen taron kara wa juna sani kan sha'anin tsaro da aka gudanar a jami'ar Middle East Technical University inda ya ce, nan da wani dan lokaci bangaren samar da makamai na Turkiyya zai samu babban matsayi da taka muhimmiyar rawa a duniya.

Ya ce, gwada harba makamin  na daga manufofin Turkiyya na nan kusa, kuma hakan nana yadda Turkiyya ke son zama babbar jagoraa duniya a kowanne bangare.

Cakir ya kara da cewa, dukkansu suna bibiyar yadda lamarin ke tafiya, an yi gwaji na farko. A shekara mai zuwa za a yi gwajin daga kan jirgin ruwa. Kuma wannan da suka samar ya dara Harpoon girma da karfin aiki. Labarai masu alaka